Amurka ta yi nasarar tare wani kuduri a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ke neman a samawa Falasdinawa fararen hula kariya.
A kuria’ra da aka jefa a jiya Juma’a, an mayar da Amurkan saniyar ware, wacce ita kadai ta jefawa kanta kuri’a.
Sai Bolivia da Kuwait da Rasha da suka nuna adawa da kudirin, yayin da sauran mambobin kwamitin 11 suka kauracewa kada kuri’ar baki daya.
Kudirin da Kuwait ta gabatar na neman a samarwa Falasadinawa fararen hula kariya, ya samu wadatattun kuri’un samun nasara, sai dai Amurka ta hau kujerar naki, lamarin da ya sa kudurin bai tasiri ba.
Sai dai ita ma Amurkan ta yi rashin nasarar cimma wani kuduri na daban da ta gabatar, wanda ya nemi a dora alhakin tashin hankalin da ya auku a kwanan nan, akan Falasadinawa ‘yan kungiyar Hamas.
Wannan shi ne karo na biyu da Amurkan ta yi amfani da karfin kujerarta a kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya, tana dakile wani yunkuri da ta ke ganin ka iya zama barazana ga Isra’ila.
Na farkon shi ne a watan Disambar bara, inda ta hau kujerar naki, kan batun neman a sa gwamnatin Trump ta janye ayyana birnin Kudus da ta yi a matsayin babban birnin Isra’ila.
Facebook Forum