Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana kyakkyawar fata kan tattaunawar da za su yi da takwaran aikinsa na Korea ta Arewa, a ranar 12 ga watan Yuni mai zuwa, yana mai cewa ana samun ci gaba a tattaunawar da bangarorin biyu suke yi wajen maido da ganawar.
A wani sakon Twitter da ya aike a daren jiya Juma’a, Trump ya ce akwai yiwuwar zai kasance a Singapore a wannan rana da aka tsayar, kuma ba mamaki ma, za a iya fadada tattaunawar har ta wuce wannan ranar.
Sabuwar matsayar da shugaba Trump ya dauka, na zuwa ne bayan da hukumomin Korea ta Arewa suka nuna sha’awarsu ta a tattauna, duk da cewa ya soke zaman kamar yadda aka tsara.
Amurka ta soke ganawar ce a ranar Alhamis, bayan abin da ta kira barazana da Korea ta arewan ke yi na ficewa daga tattaunawar, lamarin da ya sa masu sharhi ke ta tsokaci a kai.
Facebook Forum