Baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Banki Moon yace kamarin tarzoma a kasar Burundi yana firgita shi, kuma yayi Allah wadai da kashe dan wani sananen mai hankoron kare hakki da yancin jama'a da aka yi jiya Juma'a.
A wata sanarwar daya gabatar jiya Juma'a, yace gano gawarwarkin farar hula a yan makoni da suka shige, a yayinda yawancin su an kashe su babu gaira ba dalili, yanzu ya fara zama ruwan dare a unguwani da dama na Bujumbura baban birnin kasar ta Burundi.
Mutum na baya bayan da aka kashe, shine dan Pierre Claver Bonimpa mai hankoro kare hakkin jama'a wanda aka kashe shi yan sa'o'i bayan an kama shi a birnin Bujumbura. Shine mutum na biyu cikin iyalin Mbonimpa da aka kashe cikin yan makonin da suka shige.
Bugu da kari Mr Ban yayi Allah wadai da sanarwar da ake gabatarwa ko kuma kalaman da ake yi, da suka nuna alamar ana yi ne da nufin hadasa tarzoma ko tsana akan wata kabila ko wata kungiya.
Kasar Burundi tana fuskantar karin kashe kashe bayan da aka sake zaben shugaba Pierre Nkurunziza, a karo na uku daya hadasa cacar baki.
A ranar Litinin idan Allah ya kaimu akan shirya kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani taro na musamma domin tattauna kamarin tarzoma a Burundi.