A wajen wani taron koli kan harakokin tsaro da ake gudanarwa yau Assabar a Singapore, Sakataren tsaro na Amurka James Mattis ya fito fili yana jinjinawa kasar China kan kokarin da take ci gaba da yi ta hanyar aiki tareda sauran kasashen duniya akan kasar Korea ta Arewa – sai dai kuma ya soki China din kan ci gaba da take da girke sojojinta akan wasu tsibirran Bil Adama da ta shimfida, duk da adawar da sauran kasashen duniya ke nunawa, abinda yace ba abinda za’a amince da shi bane.
Mattis yace nacewar China wajen ci gaba da kirkiro wadanan tsibirran da kuma ajiye sojanta akansu mataki ne dake raunana matakan tsaro a nahiyar ta Asia.
Sai dai kuma wakilin China a wajen taron, Lt. Gen. Hei Lei, wanda har ila yau shine mataimakin shugaban kolejin kimiyya ta sojan China, ya musanta zargin na Amurka, inda ya nuna cewa China ba ta gudanarda wadanan aiyukkan ita kadai, inda yace kasar tashi ta rattaba hannu akan yarjeniyoyi sun fi 23,000.
Facebook Forum