Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Dakatar Da Harkokin Iyakarta Da Kasar Mexico


Hukumomin Amurka sun dakatar da harkokin sufuri kan iyakar Ysidro dake tsakanin San Diego da Tijuana, Mexico bayan da ‘yan ci rani suka yi kokarin bankawa ta kan iyakar jiya Lahadi.

Sama da mutane dari biyar maza da mata da kananan yara suka nemi kutsawa ta kan iyakar, suka bankade shingayen kan iyaka da ‘yan sandan kasar Mexico suka kakkafa, abin da yasa jami’an tsaron kan iyaka na Amurka suka harba barkonon tsohuwa, yayin da jiragen aikin tsaron kan iyaka masu saukar angulu suka rika shawagi a wurin.

Sakatariyar harkokin tsaron cikin gida Kirstjen Nielsen ta fada a wata sanarwa cewa, an rufe hanyar kan iyakar bisa dalilan tsaro, sakamakon yawan ‘yan ci ranin dake kokarin shiga Amurka ta barauniyar hanya.

Kamfanin dillacin labaran Reuters ya ambaci sanarwar ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar Mexico cewa, zata tasa keyar ‘yan ci rani dari biyar da suka yi kokarin ketara kan iyakar karfi da yaji. Sanarwar ta kuma kara da cewa, Mexico ba zata tura jami’an soji su sawa ‘yan ci ranin ido ba.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG