A yau Talata, ake sa ran Shugaban Amurka Donald Trump, zai duba rahotan binciken da gwamnatinsa ta gudanar, kan mutuwar dan jaridar Washington Post Jamal Khashoggi, wanda aka kashe a karamin offishin jakadancin Saudiyya da ke Santanbul a kasar Turkiyya.
Kafafen dillancin labarai da dama a Amurka, sun ruwaito jami’an tattara bayanan sirri na CIA suna cewa, Yarima Mohammeed Bin Salman ne ya ba da umurnin a kashe dan jaridar a ranar 2 ga watan Oktoba.
Koda yake, a ranar Asabar din da ta gabata, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce har yanzu ba a cimma matsaya ta karshe kan wannan batu ba.
Su dai hukumomin Saudiyya sun musanta cewa Yarima Salman, na da hannu a wannan kisa na Khashoggi, yayin da shi kuma shugaba Trump, ya kwatanta rahotanni da ke danganta Yarima Salma da kisan a matsayin marasa tushe.
Facebook Forum