Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Ce Manufar Da Ta Sa A Gaba Kan Taron Koli Da Koriya Ta Arewa Bai Canza Ba


Shugaba Trump Da Kim
Shugaba Trump Da Kim

Jami’an fadar shugaban Amurka ta White House sunce a daren gobe Talata ne shugaba Donald Trump zai baro Singapore bayan taron kolin nan na tarihji da zasuyi da shugaban Koriya ta Arewa (KTA), Kim Jong Un.

Jami’an sunce taron yana tafiya kamar yadda aka shirya amma kuma yana tafiya “cikin saurin da ba’a zata ba” a can farko.

Sanarwar ta White House tace gobe da safe ne shugaba Trump da shugaba Kim zasuyi ganawar su kadai da juna tareda masu yi musu tafinta ko fassara kawai, daga baya kuma azo a yi babban taron da zai hada da mukarrabansu kamar sakataren harakokin Waje Mike Pompeo da shugaban ma’aikatan fadar shugaban Amurka John Kelly da kuma mashawarci kan harakokin tsaro na Amurka, John Bolton.

Bayan an gama taron ne shugaba Trump zai yi wa manema labarai bayanin wainar da aka toya, sannan ya bar Singapore gobe da marece.

A da an dauka sai ranar Laraba ne Trump zai baro Singapore din.

Yau da ake jajibirin taron, jami’an Amurka na ci gaba da jadadda cewa makasudi daya suka saka a gabansu: wannan kuwa shine ganin bayan daukacin dukkan makaman nukiliya da masu linzame da KTA ta mallaka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG