Leo Sarkisian, mutumin da ya kirkiro dadden shirin nan na Muryar Amurka da ke dakko rahotanni kan wake-wake a nahiyar Afrika da ake kira “Music Time In Africa” a turance ya rasu yana mai shekaru 97
Sarkisian, ya kwashe rabin karni yana tafiye-tafiye a sassan Afirka, yana sauraron kananan mawakan yana kuma dakko rahotonni kan wasanninsu.
Wadannan rahotannin, sun kasance tushen shirin da ya fi dadewa da ake watsawa da harshen Ingilishi a Muryar Amurka.
Shi dai Sarkisian, ya kwashe shekaru 47 yana tafiya tare da mai dakinsa Mary, wacce ya aura a shekarar 1949, tare ne kuma suka rika haduwa da dubban kananan mawakan Afirka, suka kuma fito da fasaharsu idon Duniya.
Tafiye-tafiyen da ya yi, ya sa ya zama jagora cikin masanan wakokin nahiyar.
A cewar Heather Maxwell, kwararriya a fannin wake-wake, wacce kuma ita ta gaji Sarkisian, fitaccen aikin da ya yi, shi ne na nadar wakokin mawakin nan na Najeriya, marigayi Fela Kuti, gabanin ya kirkiro nau’in kade-kaden gargajiya na “Afrobeat,” wanda shi ne ya sa ya yi fice a duniya.
A shekarar 2012 Leo Sarkisian ya yi ritaya, a lokacin yana mai shekaru 91.
Facebook Forum