Yawancin hare-haren da 'yan Boko Haram suka kai kwanan nan a jihohin Borno da Adamawa sun aunasu ne kan masallatai.
Harin baya bayan nan da suka kai kan sabon masallacin Juma'an Jimeta ya hallaka mutane fiye da talatin. Na Borno da suka kai makonni biyu da suka wuce mutane fiye da saba'in suka mutu a masallacin tare da rusheshi.
Sabili da wadandan hare-haren ofishin jakadancin Amurka dake Abuja ya fitar da wata sanarwa da ta fito daga kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka John Kirby inda yake yiwa jihohin biyu ta'aziya.
A sanarwar Amurka ta yi tur da hare-haren kunar bakin wake da aka kai kan masallatan dake Borno da Adamawa. Sanarwar ta ambato kakakin yana bayyana alhini tare da mika ta'aziya musamman ga iyalan wadanda wannan aika-aikar ta rutsa dasu.
Amurka tace yin anfani da yara kanana musamman 'yan mata wajen aikasu su yi kunar bakin wake na nuna irin matakan da kungiyar Boko Haram ke dauka tana tayar da hankalin mutanen arewa maso gabashin kasar da ma zirin tafkin Chadi.
Sanarwar ta kara da cewa Amurka zata cigaba da marawa gwamnatocin kasashen dake yankin tafkin Chadi a cigaba da fafatawa da ake yi na kawo karshen aika aikar 'yan Boko Haram.
Ga karin bayani.