Fashewar ta auku yau juma’a da Asuba ne ‘yan sa’oi bayan wadansu tagwayen hare haren kunar bakin wake da aka kai a wani Masallaci dake Maiduguri babban birnin jihar Borno da ya kashe mutane talatin.
Jami’an agajin gaggawa sun bayyana yau Jumma’a cewa, ‘yan kunar bakin wake biyu sun tarwatsa kansu a cikin wani masallaci jiya alhamis da yamma a Maiduguri babban birnin jihar.
An tada nakiya ta biyu ne da nufin kashe mutanen dake kokarin kai dauki bayan fashewar farko. An tada boma boman ne lokacin da mutane suka taru suna sallar Magariba.
Mutane da dama sun raunata. ‘yan sanda sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa masallacin yayi kaca kaca.
Ko da yake kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin, kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya ta sanar da niyarta ta kafa shari’ar Islama.
Kungiyar Boko Haram ta kai hare hare kan iyakokin kasashen dake makwabtaka da Najeriya. Ranar laraba, shugaban Amurka Barack Obama ya sanar da cewa, Amurka zata tura jami’an sojinta domin gudanar da aikin sa ido da sararin sama a yunkurin dafawa kasashen Najeriya da Chadi da Kamaru da Benin da kuma Niger, da suka kafa rundunar hadin guiwa da nufin shawo kan mayakan.
Obama yace za a girke rundunar sojin Amurkan a Kamaru kuma sannu a hankali adadinsu zai kai kimanin dari uku. Wani jami’in ma’aikatar tsaron Amurka yace zasu kasance a wurin har iya lokacin da ake bukatarsu.