Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yankewa Wani Tsohon Jami'in Hukumar FBI Hukumcin Dauri


Kofar shiga shalkwatar hukumar FBI
Kofar shiga shalkwatar hukumar FBI

An yankewa wani tsohon jami’in hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari, da kuma, shekaru uku hukuma tana kyakkyawan sa ido kan al’amuransa, bayan da ya amsa laifinsa na cewa ya baiwa wani ‘dan jarida bayanan sirri.

Terry James Albury, mai shekaru 39, ya amsa laifinsa ne tun watan Afrilu, na cewa ya saci bayanan sirri na tsaron kasa kuma ya mika su ga wata kafar labarai ta yanar gizo da ake kira The Intercept.

Hukuncin da aka yanke masa bai kai wanda masu gabatar da ‘kara suka nema ba, suna mai jayayyar cewa Albury yaci amanar da mutane suka bashi, ta hanyar kwarmata bayanai har 70, kuma 50 daga cikinsu na sirri ne.

Lauyan dake kare Albury ya nemi alkali ya yanke masa hukuncin jeka gyara halinka, yana mai cewa abin da ya gano lokacin da yake jami’in FBI na tsawon shekaru biyar a matsayinsa na bakar fata, ya haddasa masa rikicewa kan ana nuna wariyar launin fata a yaki da ta’addanci da ake.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG