Ana kyautata cewa shugaban kasar Cote d'Ivoire mai ci Laurent Gbagbo ya yi jawabi ga kasa game da bukatun Kungiyar Kasashen Afirka na cewa ya mika mulki ga abokin jayayyar shi Alassane Ouattara.
Ma'aikatan diflomasiyar Afirka da jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun ce watakila ma a yau din nan alhamis da yamma Mr.Gbagbo ya yi jawabin ta talbijin.
A makon jiya Kungiyar Kasashen Afirka ta nuna goyon bayan ta ga Mr.Ouattara a matsayin mai nasara a zaben shugaban kasar da aka yi a watan Nuwamba,sannan Kungiyar ta bi sahun Kungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka,ECOWAS (CEDEAO), da kuma Majalisar Dinkin Duniya a kiraye-kirayen da su ka riga su ka yi cewa lallai Mr.Gbagbo ya yi murabus.
Mr.Ouattara ya yarda da shawarwarin da Kungiyar Kasashen Afirkar ta bayar,na karfafawa Mr.Gbagbo guiwar barin mulki a cikin lumana. Tsohon Frayim Ministan ya na yin tayin kasa gwamnatin hada kan kasa, da kafa kwamitin bin diddigi da dinke baraka, da kuma hade sojojin kasar su koma tsintsiya mai madauri daya.
Ya zuwa yanzu dai Mr.Gbagbo ya yi watsi da illahirin kiraye-kirayen cewa ya mika mulki, sannan kuma rikicin bayan zabe ya kawo fargabar cewa kasar Cote d'Ivoire na iya fadawa cikin yakin basasa.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Cote d'Ivoire ya fada a yau alhamis cewa mutane Goma Sha Takwas ne su ka rasa rayukan su a makon jiya, mutane Dari Hudu da Goma kenan su ka mutu sanadiyar rikicin bayan zabe.