Wakilin Muryar Amurka Babangida Jibril, ya zanta da ‘daya daga cikin mambobin kungiyar lauyoyin Najeriya, Barista Dan Lami Alhaji Wushishi, game da matsayin lauyoyin kan wannan takaddama da ta mamaye bangaren Shari’a a Najeriya.
Barista Dan Lami, ya bayyana cewa duk wani lauya a Najeriya bai ji dadin abin da ya faru tsakanin hukumar DSS da Alkalan da suka cafke, bisa samunsu da akayi a gidajensu da kudade da wasu kayayyaki da akace sun samesu ne ba bisa ka’ida ba.
Da farko dai kungiyar lauyoyin Najeriya NBA ta fito ta nuna rashin amincewarta ga yadda aka kama alkalan. Sai dai daga baya kungiyar ta canza matsayinta inda har ta nemi duk alkalin da ake zargi da ya ajiye aiki har sai an kammala bincike.
Duk da yake dai Alkalin kotun kolin Najeriya yace har yanzu dai hukumar DSS bata gabatar masa da wannan laifi na alkalan a gabansa ba.
Domin karin bayani.