Rundunar sojoji ta 23 dake Yola, fadar jahar Adamawa ta mika gudumawar kayan karatu ga malamai da suke karantar da 'yara 'yan gudun hijira, wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu fiyeda shekaru 6 yanzu.
Kwamandan rundunar Birgediya Janar Benson, yace baya ga yaki da 'yan binidga masu tada kayar baya, dakarun kasar suna kuma tallafawa 'yan gudun hijira ta fuskar kiwon lafiya, da ilmi, da kuma tabbatar da wadanda suka sami komawa muhallansu basu fuskanci matsi ba.
A hukumance hukumar bada agajin gaggawa watau NEMA ce take kula da 'yan gudun hijira. Mallam Sa'adu Bello yace, shirin samar da ilmi da hukumar take baiwa 'yan guudn hijiran, yana taimakwa yara masu yawa. Domin a karon farko akwai wadanda basu taba shiga makaranta ba da suke cin gajiyar shirin.
Ga karin bayani.