Hari na baya bayan nan da suka kai shine wani harin sari ka noke da suka kai wasu kauyukan karamar hukumar Madagali, dake makwabtaka da jihar Borno, inda baya ga asarar rayuka kuma suka sace Shanu tare da lalata gonaki.
Sai dai mazauna yankin sun tabbatar da cewa mayakan basu kwasa da dadi ba a hannun mayakan ‘yan sa kai na maharba da ‘yan Banga dake taimakawa sojoji. Inda sukace an kashe mayakan kusan Talatin, an kuma kama wani da rai har an mikashi ga sojoji.
Bayan da ta tabbatar da faruwar lamarin Hajiya Aisha Gombe, daya daga cikin kwamandojin ‘yan sa kai na maharba dake tallafawa a yankin tace yanzu haka suna samun nasara kan ‘yan bindigar, duk da cewa sunfi aikata barna a kauyuka domin sukan kashe mutanen kauyen baki daya su kafa tutucinsu su zauna ciki.
Har yanzu dai hukumomin tsaro a jihar Adamawa basu yi karin haske ba game da wadannan sabbin hare hare da ake kaiwa. Sai dai a wata zantawa da wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abudul’aziz yayi da kwamandan rundunar soja ta 23 dake Yola, yace yanzu haka suna samin nasara kan ‘yan bindigar, kuma yanzu babu wani yanki a Adamawa dake hannun ‘yan Boko Haram.