Rashin sanin muhimmancin kuri’a a wajen mai ita wata babbar matsala ce da aka gano cewa ta na mayar da hannun agogo baya a yunkurin damka al’amuran mulki a hannun jama’a, dalili kenan da ya sa kungiyar farar hula ta MPCR ta kaddamar da wani gagarumin shirin fadakarwa da nufin wayar da kan al’umar Nijer ta yadda zasu kare kansu daga fadawa tarkon ‘yan siyasar da suka maida cininkin kuri’a sana’a.
Dan takarar zaben ‘yan majalisar dokokin kasa a karkashin inuwar jam’iyar RSD Gaskiya, Dr Hassan Malan Gamkalley, na daga cikin ‘yan siyasar da suka halarci wannan mahawara wacce ya ce bayanan da suka fito a yayinta na fayyace zahirin abubuwan da ke faruwa a fagen siyasar wannan kasa.
Matasa na daga cikin rukunin al’uma da aka fi yawo da hankalinsu a lokutan zabe duk kuwa da cewa da bazarsu ake rawa, saboda haka tsohon sakataren kungiyar daliban jami’ar Yamai Isma’ila Mahamadou ke jan hankula game da nauyin da ya rataya a wuyansu don tabbatar da dimokradiya a kasar ta Nijer.
Kakakin hukumar zabe Nafiou Wada, da ke daya daga cikin wadanda suka gabatar da kasida, ya jaddadawa mahalartan wannan mahawara cewa hukumar CENI na ci gaba da daukar matakai don ganin zabubbukan da za a yi ranar 27 ga watan Disamba sun gudana a karkashin doka, daidai da abubuwan da kundin tsarin mulki da kundin zaben Nijer suka yi tanadi.
Saurari Rahoton Souley Mumuni Barma: