Masu sauraron labaru da shirye-shirye na gidajen rediyo na bayyana nagartaccen tasiri da rediyo ya ke yi a rayuwar su.
Wannan na zuwa ne yayin bikin ranar rediyo ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ware13 ga watan Fabrairu na ko wace shekara don gudanarwa.
Farfesa Ahmed Adamu na jami'ar NILE Abuja da masu sauraron rediyo na kungiyar Muryar Talaka a Najeriya ne ya bayyana hakan yayin gagarumin taro da suka gudanar, da ya hada masu jawabi daga jami'o'i don duba tasirin rediyo.
Kwamred Bishir Dauda daga jihar Katsina ya ce ba ya ganin akwai kafar labarun da za ta yi gogayya da rediyo wajen isar da sako.
Hakanan shi kuma tsohon ma"abocin sauraron rediyo Bello Dandin Mahe Suleja ya ce kimanin shekaru 60 ya yi ya na sauraron rediyo.
Za'idu Bala Kofa Sabuwa da ya yi fice a harkar mu'ammala da gidajen rediyo ya ce kafar ya na amfanar dukkan nau'in jama'a.
Duk da komawa yanar gizo da wasu kafafen ke yi hakan bai rage martabar akwatin rediyo ba da ya zama tamkar al'ada a tsakanin al'umma musamman na arewacin Najeriya.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:
Dandalin Mu Tattauna