Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutanen Rohingya 180 Ne Suka Rasa Rayukansu A Teku


Akalla Mutanen Rohingya 180 Ne Suka Rasa Rayukansu A Teku
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:02 0:00

Akalla Mutanen Rohingya 180 Ne Suka Rasa Rayukansu A Teku

Mai yiwuwa, nutsewar da wani kwale-kwalen ‘yan gudun hijirar Rohingya ya yi dauke da mutum 180, ya zamanto hadari mafi muni da ya auku a teku a ‘yan shekarun bayan nan.

WASHINGTON, D.C. - Lamarin ya auku ne yayin da ‘yan gudun hijirar na Rohingya, wadanda Musulmai ne, ke tserewa matsananincin halin da suke ciki a sansanonin ‘yan gudun hijira a Bangaladesh.

Akalla ‘yan kibilar ta Rohingya miliyan daya ne daga kasar Myanmar suke zaune a sansanin ‘yan gudun Hijra a Bangladesh, cikinsu har da wadanda suka tserewa hare-haren da sojojin Myanmar suka kaddamar tun a shekarar 2017.

Adadin ‘yan Rohingyar da ke ficewa daga Bandgladesh a wannan shekara ya ninku har sau biyar daga abin da aka gani a bara, kamar yadda kungoyoyin kare hakkin bil Adama suka sanar.

XS
SM
MD
LG