Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dakatar Da Sauka Da Tashin Jirage Bayan Fashewar Tayar Jirgi


jirgin MAX AIR
jirgin MAX AIR

Allah ya kiyaye aukuwar wani hadarin jirgin sama mallakin Max air bayan da tayar jirgin ta fashe da ya ke yunkurin sauka a titin jiragen saman dake babbar tashar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Matafiya da dama sun rasa yadda za su yi bayan da tayar wani jirgin sama ta fashe sannan ta kama da wuta a yayin da jirgin ke kokarin sauka a titin jirgin sama na 04/22, lamarin da ya sa aka rufe titin da jirgin na Maxair ya taso daga birnin Yola yayi saukar gaggawa a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, ta samu bayanan cewa Tawagar ma’aikatan NAIA da suka kau da jirgin daga kan tintin suna nan suna kokarin duba lafiyar hanyar tare da share shi domin sake bude titin, bisa bayanan da jaridar Daily Trust ta yi.

Kakakin hukumar tarayyar da ke kula da tashoshin jiragen saman Najeriya Faithful Hope-Iybaze, ta tabbatar cewa an kawar da jirgin akan hanya sannan kuma ta ce, suna kokarion tsaftace hanyar titin jiragen da misalign karfe takwas da kwata.

Tuni cibiyar binciken kariya ta Najeriya ta kaddamar da bincike domin gano musababin lamarin da ya auku bayan da jami’anta suka binciki jirgin kafin a kawar da shi.

Kamfanin jiragen ya tabbatar da cewa tayar jirgin ce ta fashe amma dukkannin fasinjojin da suke cikin jirgin su 144 da ma’aikatan jirgin sun sauka daga cikin jirgin cikin koshin lafiya. Kamar yadda kamfanin Air Peace ya sanar da fasinjojin da za ayi jigilarsu cewa sun soke tafiyar.

Bayan aukuwar wannan lamari da Allah ya kiyaye, an dakatar da zirga-zirgar jirage ko kuma an soke wasu a cewar wani matafiyi a Kano wanda ya ce ko da sakon sanarwa kamfanin na Maxair bai aike wa fasinjoji ba ko ta hanyar sakon ko ta-kwana ko kuma ta email.

XS
SM
MD
LG