Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afrika Ta Tsakiya Ta Kira 'Ya'Yanta Dake Gudun Hijira A Waje Su Dawo Gida


'Yan gudun hijiran Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
'Yan gudun hijiran Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Kasar Kamaru ta ce wasu ‘yan kalilan ne kawai daga cikin ‘yan gudun hijirar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dinnan 285,000 su ka amince su koma kasarsu.

Duk kuwa da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a watan Fabarairu, da kuma kwashe watanni da aka yi ana tattaunawa tsakanin Kamaru da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD), kan cewa ‘yan gudun hijirar sun ce basu da kwanciyar hankalin da zasu koma gida.

An kashe mijin Florence Yaomby mai shekaru 49 a wata musayar wuta da aka yi tsakanin ‘yan aware da sojojin gwamnati a garin Mingala na jamhuriyar Afirka ta Tsakiya shekaru hudu da suka gabata.

Ta gudu zuwa kasar Kamaru domin kare lafiyarta, inda ta zauna a matsayin ‘yar gudun hijira tun wancan lokacin.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na fama da tashe-tashen hankula tun shekarar 2013, lokacin da ‘yan awaren Seleka wadanda akasari Musulmi ne, suka kawar da Shugaban kasar wancan lokacin, Francois Bozize, wanda nan da nan ya janyo martani daga mayakan Kirista.

A watan Fabrairu, hukumomi su ka cimma yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyoyin ‘yan bindiga 14, biyo bayan tattaunawar da MDD ta shirya a Khartoum. An yi tsammanin hakan zai kai ga kwanciyar hankalin da zai kai ga yarjejjeniyar zaman lafiya tsakanin Janhuriyar Afirka Ta Tsakiya da kasar Kamaru da kuma hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD kan ‘yan gudun hijirar Afirka ta Tsakiya da ke kasar Kamaru su koma gida.

Amma ya zuwa yanzu ‘yan gudun hijira 6,000 ne kawai su ka amince za su koma. Kamar yadda Yoamby ta ki komawa Afirka ta Tsakiya, tana mai tsoron tashin hankali a wasu yankunan kasar da yaki ya ‘dai ‘dai ta.

Viviane Baikoua ita ce Ministar Harkokin Jin ‘kai da Sasantawa ta jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Ta ce kasarta tana bukatar ‘yan kasar su koma gida, domin su taimaka wajen farfado da kasar.

Wakilin hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Afirka ta Tsakiya, Buti Kale, ya ce tashin hankali ya ragu tun lokacin da aka samar da yarjejeniyar zaman lafiya, musamman ma a yankin yamma da kudu maso yamma na Afirka ta Tsakiyar.

Amma da yawa daga cikin kungiyoyin ‘yan bindigar sun ki amincewa da majalisar ministocin shugaban kasa Faustin-Archange Touadera, saboda shida ne kadai daga cikin kungiyoyi ‘yan bindiga 14 da suka saka hannu a yajejeniyar a ciki.

Masu shakkar yiwuwar yarjejeniyar Afirka Ta Tsakiya sun yi nuni da irin yarjejeniyar da aka samar a shekarar 2014 da 2015 da kuma 2017 wadanda nan da nan suka ruguje.

MDD ta ce ‘yan kasar Afirka ta Tsakiya sama da 600,000 ne har yanzu suke zaman gudun hijira a kasashe makwabta, ya yin da mutane sama da 650,000 suke zaman gudun hijira a cikin kasar.

Ga fassarar Rohotn Moki Edwin Kindzeka:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG