Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Gawarwaki 14 Na 'Yan Afrika Masu Zuwa Turai A Tekun Tunisia


Ma'aikatan ceto
Ma'aikatan ceto

Askarawan tsaron gabar tekun Tunisia a jiya Asabar sun tsamo gawarwaki 14 na bakin haure ‘yan Afrika da suka niste a cikin jirginsu dake dauke da mutane 80 a lokacin da suka taso makwabciya Libya zuwa Turai, inji hukumar Red Cross ta Tunisia.

Wasu masunta na kasar Tunisia sun ceto wasu mutane hudu amma kuma daya ya mutu a asibiti, a cewar hukumar kula da ‘yan hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a ranar Alhamis. Sauran mutane dake cike makil a cikin jirgin ruwan ana fargabar kila suma sun nitse.

Akalla bakin haure 65 da suke kan hanyarsu daga Libya zuwa Turai ne suka niste a watan Mayu da ta shude yayin da jirgin ruwansu ya yi hatsari a gabar tekun Tunisia.

Tekun yammacin kasar Libya ne inda bakin haure daga Afrika suke fara bulaguro da niyar isa Turai, sai dai adadin bakin hauren dake bi wurin ya ragu saboda kokarin da kasar Italiya tayi na hana amfani da wannan barauniyar hanya da kuma taimakon da take baiwa askarawan tsaron gabar tekun kasar Libya.

Koda yake fadar da ake gwabzawa a Libya yasa masu fasa kwaurin mutane suna shan wahala wurin bin hanya, ma’aikatan agaji na kasa da kasa sun yi kashedi cewa wannan lamari zai sa ‘yan kasar Libya su arce daga kasar su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG