Ministan Lafiyar kasar Zweli Mkhize ya fada yau Laraba cewa, Afirka ta Kudu za ta jingine shirinta na amfani da allurar rigakafin Oxford da AstraZeneca a yanzu, saboda damuwa da ta yi ko tana aiki kan sabon nau’in cutar N501Y.
Ministan lafiyar kasar ya ce masana kimiyyar kasar za su ci gaba da duba allurar rigakafin AstraZeneca da kuma bada shawara ko su yi musayar allurar rigakafin kafin lokacinta ya kare.
Kamfanin dillacin labarai na Associated Press ya rawaito Mkhize ya fada a gidan talabijin na kasar, allurar rigakafin daya ta Jonhson & Jonson tana da kyau, bisa gwaji da aka yiwa mutane dubu 44,000 a Afirka ta Kudu da Amurka da kuma Yankin Latin Amurka.
Ko da yake, har yanzu babu wata kasa da ta amince da allurar rigakafin ta Jonson & Jonson. Sai dai kamfani a makon da ya gabata ya nemi izinin yin amfni da ita na gaggawa a Amurka.
Ana sa ran Afirka ta Kudu za ta yi amfani allurar rigakafin Pfizer da wasu don taimakwa shirin rigakafin.
Afirka ta Kudu ita ce tafi kowace kasa yawan masu harbuwa da COVID-19 a Nahiyar Afirka, tare da sama da mutane 1,479,000 wadanda aka tababtar sun kamu da kuma 46,869 da suka mutu, a cewar Cibiyar Tattara bayanai ta Jami’ar Johns Hopkins.