Yayin wani taron manema labarai a da aka yi a birnin New York a ranar Juma’a, shugaban majalisar dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce “yana da matukar muhimmanci a hada kan kasar Libya.
Ya kuma nuna bukatar a tunkari hanyar samar da zaman lafiya, inda ya ce gudanar da zabe, na daga cikin wadannan hanyoyi.”
A dai karshen wani taro da aka kwashe mako guda ana yi a Geneva, wanda ya shafi batun tattauna siyasar kasar ta Libya, an zabi sabbin shugabannin gudanarwa bayan zabuka da aka yi a matakai biyu.
Mukaddashiyar wakilin Majalisar Dinkin Duniya kan Libya, Stephanie Williams, ta yi fatan ganin an samu maslaha mai dorewa, wacce za ta zamanto ta samo tushenta ne daga ‘yan kasar ta Libya.
Libya ta fada rikicin siyasa ne tun bayan da aka kawar da gwammatin marigayi Moammar Ghadafi a shekarar 2011.