Ita dai gwamnatin jihar tace ta dau wannan mataki ne domin hana wadanda ta kira bata gari shigowa shiga jihar.
Matafiya da dama ne dai gwamnatin jihar Taraba ta maida zuwa jihohinsu cikin kwanakin nan, a wani yunkuri da gwamnatin jihar tace tana yi domin tsaftace jihar daga bata gari, batun da hukumar kare hakkin dan adam ta Najeriya, National Human Rights Commission, ke cewa ya sabawa doka.
Baya ga maida matafiyan, haka nan akan wulakanta wasu da kuma karban kudade daga hannunsu kamar yadda direbobi da matafiyan da suka fada hannun jami’an gwamnatin Taraban suka tabbatarwa manema labarai.
Ita ma a martaninta, kungiyar direbobi ta kasa, NURTW, reshen jihar Taraba ta yi kirane ga shugabanin hukumomin tsaro a kasar dasu gudanar da binciken abubuwan dake wakana a jihar Taraba.
Alhaji Kabiru Muhammad Jauro, shugaban kungiyar direbobin shiya ta biyu a jihar ya ce yanzu haka wannan batu na shafar sana’ar su.
To sai dai kuma, don gano gaskiyar zargin da ake yi jami’an hukumar kare hakkin dan Adam a Najeriya, a jihar sun kai wani sumame zuwa wani shingen da ake maida matafiyan, inda jami’in hukumar a jihar Ahmad Gambo Dawood, ya ce kawo yanzu sun tuntubi jami’an gwamnatin jihar inda suka bayyana musu cewa basu da hurumin hana wani shigowa.
Kawo yanzu dai rundunan yan sandan jihar ta bakin kakakinta ASP David Misal, ta ce tana bincike to sai dai kuma gwamnan jihar Arch Darius Dickson Isiyaku ta bakin hadiminsa ta fuskacin harkokin yada labarai Mr Sylvanus Giwa, ya ce an dau wannan mataki ne biyo bayan rahotannin sirrin da suka samu na cewa akwai bata garin dake fantsamowa cikin jihar.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum