Rundunar tsaron farin kaya Civil Defense, reshen jihar Adamawa, dake kawo sulhu tsakanin makiyaya da manoma yana shiga daji ne domin zakulo masu laifi.
Yunkurin na kawo sulhu tsakanin makiyaya da manoma ya soma yin tasiri a jihar Adamawa.
Suleiman Baba jami'in hulda da jama'a a jihar Adamawa, na rundunar shi ya bayyana irin nasarorin da suke samu. A cewarsa bisa umurnin gwamnatin tarayya suka bude sashen dake shiga daji yana zakulo masu laifi, sannan akwai sashen dake kula da dabbobi da gonaki da anfanin gonaki. Akwai kuma bangaren dake warware rikici.
A cewarsa da zarar sun sami masu laifi sai su shiga batun sasantawa. Aikin da suke yi har ya sa sun samu takardar yabo daga gwamnatin jihar. Ya ce suna tare da makiyaya da manoma amma kuma suna son gwamnatin jihar ta zaburo ta sa iyaka tsakanin burtali da filin noma.
Shugabannin kungiyoyin makiyaya su ma sun yi furuci a kai. Alhaji Musa Usman daya cikin shugabannin kungiyar PULAKO ta Fulani, ya ce sau tari 'yan Civil Defense, sun je wurinsa domin sasanta rikici. Ya ce sun sasanta akan gonaki da yawa.
Shi ma Muhammad Baba, wani manomi da shanu suka yiwa barna a Yola, an sasanta dashi ba tare da zuwa gaban shari'a ba.
Sai dai sau tari kananan yara dake kiwo suke haddasa barna a gonaki kuma kusan kowane lokaci yawancinsu na cikin maye sabo da haka aka yi kira ga makiyaya su san irin yaran da suke sa kiwo.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Facebook Forum