'Yan asalin Abuja sun yi bore tare da rufe babbar hanyar da ta taso daga birnin Abuja zuwa Lokoja wadda ita ce hanya tilo da ta hada arewacin kasar da kudu maso gabashi.
Masu zanga zangar dai sun yi hakan ne domin nuna bacin ransu bisa abun da suka kira yunkurin da sojojin Najeriya ke yi na kwace masu filaye.
Wani da ya yi magana da Muryar Amurka cikin masu boren ya ce tun lokacin kakanninsu ba su taba ji an ce kasar ta sojoji ba ce.
A cewar mutumin sun yi magana da sarakunansu har magana ta kai kunnen ministan birnin Abuja.
Shi ma hakimin Zuba ya isa wurin yana bai wa matasan hakuri su bude hanyar da suka datse da hakan ya takaita zirga zirgan motoci akan hanyar.
Biyo bayan hakurin da sarkin Zuba ya ba matasan a samu an budeta bayan ta yi awa biyar a rufe.
Hakimin Zuba, Alhaji Kasimu ya ce bai ji dadin rufe hanyar ba saboda tana yiwuwa akwai marasa lafiya.
Ya kara da cewa sojoji sun basu hadin kai.
Daga furucin hakimin Zuba lallai an rubutawa ministan Abuja akan filayen kuma an kafa wani kwamiti akan filayen.
A cikin wani rubutaccen sako da kakakin rundunar sojan Najeriya, Janar Sani Usman Kuka Sheka, ya aikowa Muryar Amurka, yace sojojin suna kokarin katange filayensu ne sai su 'yan asalin Abujar suka fara bore, kuma sojojin suka dakatar da wannan aiki.
Yanzu haka dai batun yana gaban ma'aikatar raya babban birnin tarayya Abuja.
Facebook Forum