Wani rahoto mai tsoratarwa da kungiyar lafiya ta Duniya ta fitar jiya Talata, na cewa ‘daya daga cikin magunguna goma da ake sayarwa a kasashe masu tasowa na jabu ne, wanda kuma ya ke sanadiyar mutuwar dubban kananan yara, al'amarin da cikin sauki za’a iya rigakafin sa.
A yunkurin kungiyar na farko domin nazarin matsalar, masana sun sake duba wasu gwaje gwaje har guda 100 da aka gudanar tsakanin shekarar 2007 zuwa 2016, wanda ya kunshi magunguna fiye 48,000. Masanan sun gano cewa kashi 10.5 cikin 100 na magungunan na jabu ne ko marasa kyau.
An lissafa kusan kashi 65 daga cikin dari na magungunan jinyar zazzabin cizon sauro, malaria a matsayin magungunan jabu.
Kasashen da wannan lamari ke faruwa a cikinsu, suna kashe kusan dala biliyan 300 kan magunguna a duk shekara, wanda hakan ke nufin kamfanonin dake sarrafa magungunan jabu, kudin da suke samu ta kai dala biliyan 30.
A cewar wata tawaga daga makarantar koyar da kiwon lafiya da kuma nazarin magungunan kasashe masu zafi ta London, an kiyasta mutanen 116,000 dake mutuwa duk shekara a sanadiyar magungunan malaria na jabu suna kasashen yankin sahara na Afirka kadai.
Facebook Forum