Kamar yadda rahotannin suka bayyana maharan sun kai sabbin hare haren ne a rugayen Fulani dake kauyukan Bidda da Wubaka da Kaurami da kuma Ngengle dake kananan hukumomin Demsa da Mayo Belwa na kudancin jihar Adamawa wanda kawo yanzu ba’a tabbatar da adadin rayukan da suka salwanta ba.
Wadanda suka tsira da rayukansu yanzu haka suna gudun hijira a cikin garin Mayo-Belwa.
Shugaban karamar hukumar Mayo-Belwa, Hon. Muhammad Bako, ya bayyana halin da ake ciki da kuma taimakon da suka bada.
Yanzu haka dai tuni hukumomin tsaro a jihar suka yi wani taron gaggawa da jami’an gwamnatin jihar Adamawa domin daukan mataki. SP Othman Abubakar dake zama kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ya bayyana damarar da suka yi.
Cikin kwanakin nan dai rayuka da dama ne ke salwanta a Najeriya baya ga dukiyar da ake rasawa ta sanadiyar tashe-tashen hankula da ake samu a wasu sassan kasar, musamman shiyar arewa kuma wannan na ma zuwa ne yayin da ake fuskantar zaben shekarar 2019.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum