A rahoton da kwamitin karbar mulki ta fitar a jihar Adamawa, daya daga cikin jihohin da aka samu sauyin gwamnoni, an bankado tulin bashin da ake bin jihar na sama da biliyan 115, batun da gwamnatin dake shudewa ke cewa an shafa mata kashin kaji.
Rahoton karbar mulkin da sabon gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri ya kafa ta ce, ta bankado wasu almundahana da suka shafi kudaden fansho, giratuti da kuma dinbin basussukan da ake bin jihar Adamawa a yanzu wanda suka ta sarma Naira biliyan 115, wanda mafi tsoka wanda gwamnatin dake shudewa ne ta ciyo.
Da yake mika rahoton nasu Alhaji Aliyu Ismaila Numan dake zama shugaban wannan kwamitin, ya ce sun bankado ababe da dama da na iya kaskara gwamnati muddin ba'a dau mataki ba.
To sai dai a martanin da gwamnan jihar mai barin gado Sanata Muhammadu Umaru Jibrilla Bindo ya maida ta bakin kwamishinan kudi Alhaji Sali Yunusa, ya yi fatali da abubuwan da yan kwamitin suka ce sun bankado.
Kawo yanzu sabon gwamnan jihar mai jiran gado Ahmadu Umaru Fintiri ya ce za'a aiwatar da rahoton kwamitin don kawo ci gaba ba don cin zarafin wani ba.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum