Akalla, an kashe kwanaki bakwai a jere, kullum sai ‘yan bindiga dadi sai sun tada gari ko sun kona gari a jihar Katsina musamman a yankin Batsari inda wannan abu yafi tsamari, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin tsananin fargaba.
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya gana da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari kana shugaban kasar ya tura wani kwamitin mai karfin gaske karkashin jagorancin babban hafsin hansoshin rundunar sojan Najeriya, Janar Abayomi Gabriel Olonisakin da shugaban ‘yan sandan kasar da su je ga yanda lamarin yake.
Gwamnan na Katsina yace an samu karin karfin gwiwa saboda yanzu haka mun ‘yan Ktsaina mun riga mun tura mutane suna taimakawa kuma zasu je dukkan wuraren da ake fama da tashin hankali musamman kananan hukumomin Btsari da Kankara inda abin yafi tsanani.
Amma a cewar mutanen karamar hukumar Batsari ta bakin Lawal Sani daya mai magana da yawun su, yace su basu gamsu da turo musu irin wannan kwamiti ba, so suke su gani a kasa. Lawal sani yace idan shugaban kasa na bukatar ya san abin dake faruwa ba kwamiti zai turo ba, sai ya tuntubi hakimai da masu unguwar da ake wannan abu.
Daga Abuja wakilinmu Hassan Maina Kaina na dauke da kari bayani:
Facebook Forum