Wani rahoto da cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasa ta NCDC ta fitar a baya-bayan nan ya nuna cewa adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya a yanzu ya kai 174.
Sabbin alkaluman da cibiyar ta fitar sun nuna cewa, a karon farko jihar Akwa Ibom ta samu wadanda suka kamu da cutar su 5 a cikin sabbin mutane 23 da suka kamu da cutar ta coronavirus. A yayin da aka samu karin mutum 9 a jihar Legas, 7 kuma a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Kawo yanzu, cibiyar ta ce tana neman wasu mutane kimanin 4,000, wadanda ta yiwu suna dauke da cutar ko kuma sun yi mu’amalla da wadanda ke dauke da cutar.
A sanarwar da ya fitar, babban daraktan cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) Dr. Chikwe Ihekweazu, ya ce yanzu haka a kowacce rana ana samun karuwar mutanen da ake gwadawa daga 500 zuwa 1,000 domin tantance ko suna dauke da cutar ko a'a.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Babangida Jibrin.
Facebook Forum