Gwamnatin kasar Kamaru na ci gaba da yakar yaduwar annobar cutar coronavirus, a yayin da a yanzu haka cutar ke kara yaduwa a cikin al’ummar kasar.
Duk da irin dokar da hukumar lafiya ta sanya, Ministan Lafiyar Kamaru, Manaouda Malachie, ya ce wadanda suka kamu da cutar a kasar a yanzu haka sun zarta 700. Sannan mutane 10 sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar.
Wasu daga cikin ‘yan kasar sun nuna rashin gamsuwarsu da yadda gwamnatin kasar take kula da lamarin, wasu kuma sun yaba wa gwamnatin.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Awal Garba.
Facebook Forum