Tun a shekarar 1897 da aka gano tare da fahimtar sababin cutar maleriya ake kokarin daukar matakan yaki da cutar, inda saura kiris da a a cikin shekarun 1950 an kawar da ita.
Sai dai matakan da ake daukawa na yaki da cutar basu yi tasiri sosai ba saboda kasawar kudin da ake bukata don cigaba da yakin, lamarin da ya kawo mu ga wannan matsayin da muke a yau dangane da cutar ta maleriya.
Wani rahoton Global Data Epidemologist ya kiyasta cewa kashi 70 a cikin dari na mutuwar yara kasa da shekaru biyar daga cutar ta maleriya ne. Cutar Maleriya na kassara tarin kasashen Afrika a kan kudi da ya kai dollar Amurka billiyan 12 a duk shekara.
Hanya daya ta yakar cutar ta cizon sauro ita ce gwamnatoci a fadin duniya su samar da isasshen kudin tallafawa shirin yaki da cutar, da cigaba da ilimantarwa a kan kiwon lafiya tare da waye kan al’umma su fahimci yadda matsalar take.
An soma kokarin yakar cutar maleriya a Ghana ne a cikin shekarun 1950 da zummar rage barnar da cutar ke yi . Shirin yaki da cutar maleriya na kasa ya amince sashin kiwon lafiya kadai ba zai iya magance maleriya ba, a don haka ana bukatar dabaru iri iri da suka hada da fesa maganin kashe kwari don kashe sauro, da bayar da rigakafin maleriya da kuma inganta tsarin magudanan ruwa.
Daga birnin Accra ga Ridwan Abbas da karin bayani:
Facebook Forum