Ana tuhumar Bashir, wanda ya shugabanci Sudan na tsawon shekaru 30 da mallakar kudin kasashen waje ba bisa ka'ida ba da kuma karbar kyaututtukan ba bisa ka'ida ba.
Lauyan Bashir ya fadawa Muryar Amurka cewa tsohon shugaban yana burin zai ci nasara akan laifin da ake zarginsa da aikatawa na cin hanci da rashawa.
Lauyan yake cewa: "Wannan lamari ne na siyasa saboda mutane suna cewa shugaban ya saci kudin kasar kuma ya fita da shi daga Sudan. Abin da kafofin watsa labarai ke fada kenan amma mun fadi wani abu na daban a gaban kotu, kuma har zuwa yanzu babu abun da aka ambata a ciki.”
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta tuhumi tsohon shugaban da aikata laifukan yaki, laifukan cin zarafin bil adama da kisan kare dangi a lokacin yakin da aka kwashe shekaru ana yi a yankin Darfur na Sudan.
Facebook Forum