Tsohon Shugaban kasar Sudan, Omar al-Bashir, ya gurfana a gaban kotu don fuskantar tuhumce-tuhumce kan almundahana, watanni hudu bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatinsa.
Bashir, wanda ya mulki Sudan na tsawon shekaru 30, an tuhume shi da mallakar kudaden waje da kuma kabar kyaututtuka ba bisa ka’ida ba.
Bisa ga bayanin wani jami’in bincike wanda ya yi bayani ma kotun, Bashir ya ce ya karbi tsabar miliyoyin daloli daga kasar Saudiyya.
Mazauna birnin Khartoum da dama na bakin ciki da jinkirin wannan shari’ar, da dama daga cikinsu na cewa matakin da aka dauka bai wadatar ba, kuma an makara.
Facebook Forum