Kwararowar mazauna yankunan karkara cikin birane abu ne da kan iya mayar da hannun agogo baya, ga kokarin shawo kan matsalar rashin tsaro a Najeriya.
Akan haka ne wasu ke ganin lokaci yayi da ya kamata gwamnati ta sauya salon tunkarar matsalar rashin tsaro, ta yadda zata leka duk wata kafa da zata iya ruruta wutar rashin tsaron.
Yankunan karkara sune sahun gaba wajen noma abinci wanda jama'ar yankunan zasu ci, da kuma fitarwa zuwa birane har a samu wadata kasa da abincin.
Sai dai saboda wasu dalilai da suka hada da na rashin isassun abubuwan more rayuwa, da neman kyakkyawar rayuwa kan sa mazauna yankunan yin kaura zuwa birane, abinda ke kawo koma baya ga noma, wasu na ganin yana barazana ga harkar tsaro.
Abubakar Mailato, shine shugaban kungiyar matasa mai rajin wanzar da zaman lafiya, da kawo sulhu a cikin al'umma, wadda ta gudanar da taron jan hankali, akan illolin kwararar mazauna kauyuka zuwa birane.
Ya ce "Babbar matsalar ita ce yadda matasa basu maida hankali ga noma, da yawan matasa suna sha'awar matasan da ke birni ne, suna ganin yadda suke walkiya, abun yana basu sha'awa, don haka sai suga cewar suma bari su yi bala guron, suna ganin cewar noma aikin wahala ne."
Ya kara da cewar, da yawa zakaga matashin kauye ya baro kauyen ya tare a birni da mata da yara amma babu sana'a mai kwari.
Comrade Ahmad Sarki matashi ne a Sakkwato Wanda ke ganin lokaci yayi da ya kamata matasa su kara maida himma ga bayar da gudunmuwa wajen warware matsalar rashin tsaro a Najeriya.
Ya ce "Duk wani matashi mai kishin kasa tai, ya kamata ya shiga a yi da shi wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro da ta yi katutu a cikin jama'a."
Masana halayyar Dan adam kamar Farfesa Tukur Muhammad Baba na ganin cewa ko bayan neman abubuwan more rayuwa rashin tsaro ma ya taimaka gaya ga kwararar mazauna karkara zuwa birane.
Yana ganin cewar "da yawa mazauna karkara sukan garzaya birane su kwana kana idan gari ya waye sai su koma kauyukan, don neman kare lafiyar su a dai-dai lokacin da tsaro ke kara tabarbarewa a yankunan karkarar."
Da yake hukumomi na ta fadi-tashi wajen shawo kan matsalar rashin tsaro a Najeriya, yin amfani da shawarwarin masana kan iya taimakawa ga samun biyan wannan bukata.
A saurari rahoton Muhammad Nasir cikin sauti.
Karin bayani akan: barazana tsaro, Sakkwato, Nigeria, da Najeriya.