Da ya ke jawabi a yayin da jakadan kasar Chadi a Najeriya, ya ziyarce shi a
ofishinsa da ke Abuja, ministan tsaron Najeriya Manjo Janar Bashir
Salihi Magashi ya ce yanzu ne lokacin da ya kamata a kara hada hanu irin
na karfin soja da nufin tunkarar mayakan Boko Haram gadan-gadan a irin
salon nan na "a yi ta ta kare."
Janar Bashir Magashi ya ce ta hanyar aiki tare tsakanin kasashen yankin tafkin Chadi, za a iya kawo karshen 'yan ta'addan yankin baki daya musamman ganin cewa shelkwatar rundunar dakarun yankin baki daya na da mazauni a birnin N'djamena, da ke karkashin jagorancin wani babban hafsan Najeriya Manjo Janar Ibrahim Manu Yusuf. Don haka ministan ya nemi a nuna da gaske a ke yi, in dai ana son ganin karshen wannan yaki.
Ministan tsaron Najeriya ya tabbatar wa jakadan na Chadi cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai kara taka rawa wajen ganin an kara tallafa wa dakarun MNJTF don kawo karshen 'yan ta'addan.
Tun farko cikin jawabinsa, jakadan Chadi a Najeriya Ambasada Abubakar Saleh Chachaimi, ya tabbatar da cewa kasarsa za ta hada kai da Najeriya ta fuskar tsaro, ya na mai cewa shugaba Idriss Derby ya tabbatar wa shugaban Najeriya cewa daga yanzu Chadi a na ta bangaren za ta yi duk iya kokarin ta wajen kawo karshen safarar makamai akan iyakokin kasashen biyu, sannan kasarsa ba za ta bari ya zamanto nan ne mafakar 'yan Boko Haram ba.
Jakadan na Chadi a Najeriya ya ce shugaban kasarsa ya nemi shugaba Buhari ya taimaka ya bude kan iyakar kasashen biyu ganin cewa tattalin arzikin Chadi ya ta'allaka ne akan ruhin tattalin arzikin Najeriya.
Kwararre kan harkokin tafkin Chadin Dr. Hussaini Hassan, na ganin ire-iren kananan kurakuran da ke faruwa cikin hadakar na iya sa Najeriya ta nemi cikakken hadin kan Chadi ganin mayakan Boko Haram na gallabar Najeriya ta wannan yankin.
Saurari karin bayani cikin sauti: