Kungiyar Alkalai ta SAMAN ce tayi kiran wannan yajin aiki da nufin nuna rashin amincewa da dokar, wadda aka kirkiro ta a shekarar 2003 zuwa 2004. Wadda Ministan Shari’a ke da wuka da nama game da makomar Alkalai a kan aikinsu.
Mataimakin magatakardar kungiyar SAMAN, mai Shara’a Nuhu Abubakar, yace sunga cewar wannan doka wata babbar barazanace domin zata iya karya lagon masu shari’a.
A yinin yau dai an rufe kotuna a Nijar domin wannan yajin aiki, abinda ke nufin yayi tasiri sosai akan sha’anin shari’ar kasar Nijar.
Takun saka tsakanin Alkalai da hukumomin Nijar ba wani sabon lamari bane, misalin sabanin da aka samu a farkon shekara ta 2015, lokacin da Alkalai suka bukaci shugaban kasa da ya tunkuda musu keyar Ministan cikin gida na wancan lokaci saboda zarginsa da yiwa sha’anin Shari’a karan tsaye, sakamakon wasu kalaman da ya furta wadanda alama ce ta nuna rashin gamsuwa da shari’ar nan ta Jarirai da ake yiwa tsohon kakakin majalisar dokokin kasa Hamma Amadou ke wakana.
Domin karin bayani.