Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Illar ta'adanci akan ayyukan yawon bude ido a kasashen yammacin Afirka renon Faransa


Mahammadou Issoufou mai masaukin baki
Mahammadou Issoufou mai masaukin baki

Makasudin taron kasashe takwas renon Faransa daga yammacin Afirka shi ne tattauna matsalolin dake barazana ga ayyukan yawon bude ido wanda ya fada cikin wani hali sakamakon raguwar masu yawon bude ido saboda ta'adanci a wasu kasashen yammacin Afirka.

Kasashen sun lura cewa adadin mutanen dake zuwa ganin abubuwan tarihi ya ragu ainun tunda aka soma samun hare-haren ta'adanci a wasu kasashe irin su Mali, Nijar, Burkina Faso da Ivory Coast.

Galibin hare-haren ana aunasu ne akan wuraren shakatawa da otel otel kamar yadda suka faru a Ivory Coast da Mali cikin 'yan kwanakin nan.

Aisha Sale Musa darakta a ma'aikatar bunkasa yawon bude ido ta kasar Nijar tace a taron suna son su dauki manyan matakai saboda yadasu a duk fadin duniya tare da yin bayanin cewa babu ta'adancin a kasashensu. A nasu yankin ta'adanci jefi jefi ne ba kaman wasu kasashe ba. Tace mutane na iya zuwa kasashensu domin a hankali kwance suke.

Ta kira gwamnati ta taimaka masu da fadakar da kawunan takwarorinsu na kasashen da suka yiwa 'yan kasashensu kashedin zuwa yammacin Afirka. Ta nemi a cirewa kasar Nijar sunan cewa kasar ta'adanci ce.

Su ma masu kira kayan hannu suna cikin wadanda suke fuskantar koma baya a harkokin cinikayya sakamakon rashin samun 'yan yawon bude ido a kasar ta Nijar.

Ahmadu Malam Ali sakataren masu sana'ar hannu da kere-kere yace masu yawon bude ido da suke zuwa Nijar sun ragu sosai. Yace tunda rashin tsaro ya addabi kasar sakamakon aika aikar 'yan Boko Haram ayyukan yawon bude ido suka tabarbare.

Wakilin kasar Mali yace saboda harakar tsaro sun samu koma baya a ayyukan yawon bude ido. Yace wajibi ne kowa ya tashi tsaye a yaki matsalar tsaro.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Shiga Kai Tsaye

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG