Shugaban kwamitin kulawa da ‘yan gudun hijirar Alhaji Sani Zaure, shine ya shaidawa manema labarai hakan lokacin da ya ziyarci garin Danbuwa dake jihar Borno, tare da sauran mambobin kwamitin na sa don ganewa idanunsu irin halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki.
Yace sun dai fahimci akwai matsaloli da dama da ‘yan gudun hijirar ke fuskanta, musamman ma wadanda ake fito da su a baya bayan nan da ‘yan Boko Haram suka yi garkuwa da su sakamakon irin halin da suka shiga na matsanancin yunwa.
Kididdigun dake fitowa na baya bayan nan suna nuna cewa fiye da yara Dubu Hamsin ne suke fama da karancin abinci, wanda kuma hakan yake bukatar tallafin gaggawa wanda idan ba dauka ba hakan na iya sanadin rayukan yaran.
Wasu daga cikin ‘yan gudun hijira da yanzu haka ke samun mafaka a garin Danbuwa sun bayyanawa wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda, irin halin da suke ciki da ma irin bukatun da suke mikawa gwamnati da ma kungiyoyi masu zaman kansu, don kawo musu agajin gaggawa kan halin da suke ciki.
Saurari rahotan Haruna Dauda.