Ma'aikatan sun killace kofofin shiga harabar gidan gwamnatin jihar ta Adamawa amma a cikin lumana suna dauke da kwalayen dake kira a biyasu domin a fitar dasu daga yunwa da fatara.
Ma'aikatan sun ce basu amince da rashin adalci ba saboda su da iyalansu sun tagayyara, har yunwa zata kashesu, injisu. Dalili ke nan da suke bukatar gwamnatin Adamawa ta biyasu albashinsu na shekaru biyu da watanni biyu. Wato watanni 26 ke nan gwamnati bata biyasu ko kwandala ba.
Wasu cikin ma'aikatan sun bayyana irin halin da suka shiga. Malam Inusa Adamu yace shekaru biyu ke nan da aka daukesu aiki amma har yanzu ba'a biyasu ba. Yace sun bi duk hanyoyin da suka kamata su bi domin a ji kokensu amma hakonsu bai cimma ruwa ba. Suna aiki da marasa lafiya dare da rana amma an yi watsi dasu. Idan gwamnan yana aiki domin Allah ne kamar yadda yake ikirari to kamata ya yi ya dubesu da idon rahama.
Ma'aikatan sun ce wasunsu sun rasa 'ya'yansu. Wasu kuma an koresu daga gidajen haya. Wasu ma 'ya'yansu basa makaranta domin babu kudin biya.
Bincike ya nuna sau biyu aka tantance ma'aikatan amma gwamnati ta kasa sanin sahihan ma'aikatanta.
Barrister Musa Kaibo shugaban ma'aikatan jihar yace yanzu suna cikin shirin fita su tabbatar da wadanda aka daukesu a zahiri. Yace yawancin masu surutun basu ne ma'aikatan ba. Ma'aikatan kiwon lafiya na zahiri suna asibitoci suna aiki. Masu zanga zangan waus ne suka sasu. Wasu kuma 'yan makaranta ne, inji Barrister Kaibo.
Ga karin bayani.