Kasuwar wacce ake yiwa lakabi da kasuwar Dan Jabalu, dake tsohuwar kasuwar Sokoto makekiyar kasuwa ce mai shagunan sama hawa guda wadanda suka yi da’ira tare kuma da wasu shagunan a tsakiya.
Duk da cewa hukumar kashe gobara sun kai dauki, amma hakan bai hana wutar zagaye daukacin shagunan ba, lamarin da yasa wasu masu shaguna suka yi zargin sakacin hukumar da munanar lamarin.
Malam Abdulrahaman Mu’azu Dan Jabalu ya ce sakacin gwamnatin jihar Sokoto ne ya jawo masu wannan mummunar asara domin babu hukumar kashe wuta, domin a cewar sa da ankawo hukumar ta kawo dauki da an shawo kan gobarar.
A daya bangaren kuma, wasu daga cikin masu shagunan sun dora laifinne akan jami’an tsaron da suka tare su, da hana su kaiwa ga shagunansu tun kafin wutar ta kaiga kama masu shaguna.
Duk da shike babu tabbacin sanadiyyar gobarar, jama'a da dama sun alakanta ta da wutar lantarki.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna daga Sokoto.