Philip Alston, wanda masani ne gameda fannonin talauci da hakkokin Bil Adama, yace wannan matsayin na MDD “abin kunya” ne.
A rahoton da ya aikawa MDD din, Alston yace idan har ita kanta majalisar ba zata sa kai, ta dauki alhakkin wannan bala’in ba, bai kamata ta rinka matsawa wasu kasashe daukar nauyin taka hakkokin bil adama da ake a cikin kasashen nasu.
Ana dai zargin cewa cutar ta kolera ta bazu a kasar Haiti ne a sanadin sharer da sojojin kiyaye sulhu na MDD na kasar Nepal suka zuba ne a cikin koguna da gulaben Haiti.
Har yanzu ma ance kowane mako, mutane 500 ke kamuwa da cutar Kolera din a kasar.