Masu kwallon tsoffin mayakan kungiyar al-Shabab ne, kungiyar dake da alaka da kungiyar al-Qaida wadda aka kafa shekaru goma da suka gabata. Kungiyar ta al-Shabab tayi mugun fafatawa na ta’adanci da gwamnatin Somalia.
Mutanen da suka fice daga kungiyar an zabosu ne domin su ci gajiyar wani shirin sake masu tunane ko akida da Majalisar Dikin Duniya ke marawa baya maimakon a kaisu gidan kaso.
Wani da aka bashi suna Abdi domin a kare mashi sunasa na ainihi, ya bayyana irin abubuwan da ya gani lokacin da yake cikin kungiyar. Yace “zaka ji bam ya tashi amma baka so ba kuma ya kashe mutane da dama. Shugabannin sukan yi fada tsakaninsu. Kana ta rike duk wadannan abubuwa a zuci. Wani zibin kuma kwasam saisu canza ra’ayinsu ba bisa wani dalili ba”
Abun da ya canzawa Abdi tunane ya faru ne lokacin da shugabannin al-Shabab suka haramta masu yin kasuwanci. Shi kuma matashi ne a lokacin saboda ya shiga kungiyar ne bayan sojojin Habasha sun kashe mahaifinsa yayina da suke fafatawa da kungiyar al-Shaba.
A cewarsa “na yi hasarar shekaru shida. Sa’o’ina da nake tare dasu a makarantar sakandare, yanzu suna jami’a. Suna gari. Kuma yanzu idan an gansu suna da fatan alheri. Amma kafin na cika shekaru 30 ina fatan zan cimmasu”.
A kowace rana wadannan mayakan al-Shabab da suka tuba suna daukan daratsin koyon karatu, da na iya wasu ayyukan rayuwa da azuzuwan addini. Da taimakon cibiyar da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya, su kan rubuta tsarin kafa kasuwanci da zasu yi dogro kansu bayan sun kammala horon da suke samu. Manufar itace su koma da rayuwarsu cikin jama’a kamar kowa.
Amma har yanzu basu tsira ba domin kodayaushe Abdi na samun barazanar kasheshi ta wayar tarho. “yace ko kadan ba zan iya zuwa inda ‘yan al-Sahabab suke ba, kuma idan na shiga gari, jama’a na shakkata, suna ganin basu tsira ba. Saboda haka abun da yafi kyu shi ne na cigaba da zama a nan har lokacin da al’umma zasu fahimta su san mu su wanene”, inji shi.
A cikin mutane 160 dake cibiyar 40 cikinsu na zaune ne a dakunan kwana dake cibiyar sauran kuma suna zama da ‘yanuwansu ne cikin gari.
A cibiyar mazan su ne suke dafa wa kansu abinci kana su ci tare, su huta tare su kuma yi wasa har da kallon talibijan.
Shirin na daukan lokaci saboda har yanzu akwai masu tsatsauran ra’ayin addini.
Malaminsu da ya nemi Muryar Amurka ta sakaya masa suna saboda dalilan tsaro yace “Mu kan fadawa masu tsatsauran ra’ayi, cewa mu zauna mu yi nazari tare daga Kur’ani da Hadith tunda dukanmu musulmai ne. Idan naka fasarar ta fi tawa sai mu yadda tare. Idan kuma tawa ce tafi sai mu bita”.
Kawo yanzu dai babu wanda ya kammala daga cibiyar ta Baidoa da ya koma cikin kungiyar al-Shabab kamar yadda shugabannin cibiyar suka bayyana.
Tun shekarar 2013 daruruwan mayakan al-Shabab sun fice daga kungiyar. Kungiyar ma ta ce kimanin 10,000 ne suka fice . Amma tana cigaba da daukan sabbin mayaka tare da kai munanan hare-hare a Somalia da makwafciyarta Kenya.
Akawi rudani dangane da yadda ake zaban wadanda zasu shiga horon da wadanda ake kaiwa kurkuku daga mutanen da suka fice daga al-Shabab. Kuma mazauna garin na mamakin yadda tsoffin ‘yan ta’ada ke samun irin taimakon da su basu samu ba.
Cibiyar ta Baidoa maza kawai take dauka. Wasu dake cibiyar yanzu sun shaidawa Muryar Amurka cewa akwai wasu da suke da aure suna cikin kungiyar. Suna son su fice amma basa son su bar matansu baya.
Amma Patrick Loot wanda ya tsara shirin a matsayinsa na jami’in Majalisar Dinkin Duniya yace cibiyar tana da mahimmanci
Yace shirin “ya ba wasu dake cikin kungiyar al-Shabab tabbacin samun hanyar tattaunawa da gwamnati su ce ‘bari mu yi magana kan zaman lafiya’, kuma suna hulda kai tsaye da shirin saboda haka wannan shirin abu ne babba”