Wannan ne karon farko da aka ba da rahoton cewa ‘yan awaren sun yi amfani da bama-bamai tun bayan da aka fara wannan yakin shekaru uku da su ka gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane wajen 2,000.
Mutane wajen 200 da aka raba da muhallansu a sashin Ingilishi na kudu maso yammacin kasar Kamaru sun hadu jiya Lahadi a birnin Yaounde don yin nazarin karuwar tashe-tashen hankula cikin watan da ya gabata. Sun ce hare-haren da aka kai garuruwan Tinto da Kembong da Enyang, wuraren da sojoji su ka ce na ‘yan tawaye, ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 17.
Wani malamin makaranta mai suna Nestor Orock, wanda ya tsere daga yakin da ake yi a Tinto shekara guda da ta gabata, ya ce na baya bayan nan a kashe-kashen da aka yi shi ne wanda aka yi ranar Asabar, lokacin da bama bamai ya tarwatsa wata motar ‘yan sanda a Eyumojock. Ya ce wasu da su ka so dawowa gida sun tsorata da wannan.
Ministan Sadarwar kasar Kamaru kuma mai magana da yawun gwamnati Rene Emmanuel Sadi ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce ‘yan sanda sun je Manyu ne aikin tabbatar da zaman lafiya.
Kasar Kamaru na zargin wasu ‘yan kasar mazauna kasashen waje da daukar nauyin ‘yan tawayen da kuma tara masu kudaden sayo makaman yaki.
A baya bayan nan ‘yan tawayen sun yi ta amfani da kafafen sada zumunta wajen nuna hotunan irin bindigogi da bama-baman da su kace sun sayo kuma har sun yi fasa kwabrinsu zuwa cikin kasar.
Mai sharhi kan al’amuran siyasa, dan asalin kasar Kamaru, Nelson Arrey, wanda ke Jami’ar Ndjamena ta kasar Chadi, y ace daga yanzu kar kasar Kamaru ta yi wargi da batun karfi da kuma makaman ‘yan tawayen, bisa tsammanin cewa bas u da isassun kayan yaki.
Tashe-tashen hankulan na arewa maso yammaci da kudu maso yammacin kasar ta Kamaru, sun kazance ne a ranar 1 ga watan Oktoba na 2017, lokacin da ‘yan awaren maso dauke da makamai su ka yi shelar kafa abin da su ka kira, ‘yantattar kasa mai amfani da harshen Ingilishi.
MDD ta kiyasta cewa mutane sama da 530,000 ne aka raba su da muhallansu tun bayan da yakin ya barke. Ta ce mutane wajen miliyan 1.3 na bukatar agaji.
Domin karin bayani saurari rahotan cikin sauti.
Facebook Forum