Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamus Ta Mika Taimako Ga Gidajen Yarin Najeriya


Gidauniyar 'Konrad Adenauer Stiftung' ta kasar Jamus ta shirya wani taron wayar da kan masu mulki a kasa.

Taron zai taimakawa Najeriya wajen gano matsalolin da ke fuskantar gidajen yari, tare da taimakwa wajen canza yadda ake gudanar da su domin a samu nasarar gyara halayen Fursunoni ba tareda karya doka ba.

Rahotanni da wasu kungiyoyin kasashen waje da ta 'Amnesty International' suka ruwaito akan wani bincike da suka gudanar akan gidaje yarin Najeriya, ya jawo hankalin gidauniyar Konrad Adenauer har ta shirya taron da yayi dalilin hada kai don kare hakkin bil Adama, da na tabbatar da walwalar fursunoni da kuma na jami'an kula da gidajen yarin.

Jami'in gidauniyar Vladimir Kreck, ya ce sun lura cewa idan aka duba gidajen yari a kasar Amurka, ko kasashen Turai, za a ga banbancin su da wadan da ke Najeriya, wajen tsafta da kyautata yanayi da kuma yadda ma'aikatan ke kare hakkokin 'yan jarum.

Kreck, ya ce niyyar gidauniyar shi ne ta kawo masu ruwa da tsaki a rumfa guda, sannan ta taimaka masu ta hanyoyin wayarda kai a hanyoyin zamani da ma'aikatan za su yi amfani da su, wajen cimma burin gyara da warware matsaloli a saukake.

Shugaban hukumar kula da gidajen yari ta kasa Ahmed Jafar, ya ce tuni har gwamnatin Najeriya a karkashin shugaba Muhammadu Buhari ta bada izinin daukan matakan rage cinkoso a gidajen yari, domin an fara gina guda daya wanda zai dauki yawan fursunoni dubu 3 ba tareda sun samu matsala ba.

Shugaban gidauniyar a jihar Kano, Mohammed Jamo Yusuf, ya yaba da yunkurin da gidauniyar Konrad Adenauer ta yi wajen taimakawa Najeriya, a fannin jin dadin fursunoni tare da kira ga wasu kungiyoyin da su bi sawu.

Ga cikakken rahoton wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG