Tashin bom din ya farune a kan babban titin zuwa garin Gubio, inda aka ce bom din ya tashi da wasu mutane dake cikin wata mota da ake zargin ta fito ne daga cikin daji, suna tunkarar zuwa garin Gubio.
Wannan shine karo na Uku a jere da ake samun tashin boma bomai a cikin garin Maiduguri, wanda kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane da yawa wanda suka hada da maza da mata da kuma kananan yara.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, Mr. Victor Iseku, ya aikawa manema labarai ta hanar kafar sada zumunta whatsapp, na nuni da cewa bom din ya tashi ne dab da wajen wani binciken ababen hawa da jami’an sojoji ke yi a mashigar Maiduguri daga garin Gubio. Sai dai sanarwar batayi karin haske game da mutanen Hudu da suka mutu ba.
A dai dai wannan lokacin ne kuma, jami’an rundunar hadin gwiwar tsaro na Multi National Joint Task Force, suka fitar da sanarwar cewa wasu ‘ya ‘yan kungiyar Boko Haram din su 240 sun mika kansu ga jami’an sojan Najeriya a ranar Litinin din data gabata. Haka kuma mutanen sun mika makamansu kafin su mika kansu.
Sanarwar ta kara da cewa kwamandan rundunar gamayyar sojojin Majo Janal Lamidi Adeosun, ya tallafawa da mutanen da kayayyakin abinci da kuma wasu ‘yan kudaden da zasu tallafawa kansu da iyalansu.
Domin karin bayani.