Taron dai yada hancin duk shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, tun daga matakin mazaba har ya zuwa matakin jiha ta Kano.
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, yace tabarbarewar tasirin jam’iyyun siyasa bayan kammala zabe, da kuma rashin biyan akidun jam’iyu a zabebbun shugabanni na daga cikin na daga cikin mayan dalilan shirya taron bitar. Gwamna Ganduje yace sun taru ne domin karfafa jam’iyya don ganin tana da rai a koda yaushe.
A daya bangaren kuma, ‘yan siyasa da suka yi jawabai a gurin taron sun nuna biyayyarsu ne ga gwamna Ganduje, hakan yasa wakilin Muryar Amurka Umar Faruk ya tambayi gwamna Ganduje ko taron na da alaka da tankiyar mallaka da shugbancin jam’iyyar dake tsakaninsa da tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso?
Inda yace babu shakka ana rigimar jam’iyya a Kano, amma karshenta yazo tunda mutum biyu jam’iyya ta kora, kasancewar shugaban jam’iyya da sakataren jam’iyya suna zagon kasa ga gwamnatin jihar Kano, wanda hakan yasa sauran shugabanni sama da 50 suka ce sun kore su.
A taron dai an gayyato shehunnan da sauran masana sha’anin siyasa da dimokaradiyya, wanda suka gabatar da kasidu kusan 15 a lokacin taron bitar, mafi akasari dangane da ayyukan jam’iyyukan siyasa da akidojinsu da kuma rawar da suke takawa wajen tafiyar da mulkin dimokaradiyya.
Domin karin bayani.