A cikin wata kasida mai shafuna 12 da ta gabatar jiya, kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta bada misalin abinda ya sami wasu mata 43 da aka ajiye a wasu daga cikin sansanonin ‘yan gudun hijira guda 7 dake Maiduguri, hedkwatar jihar Borno kuma inda daga nan ne kungiyar Boko-Haram ta samo asali a shekarar 2009.
Hudu daga cikin matan sunce manyan jami’an dake kula da wadanan sansanonin sun bugar da su da ababen sa maye kana suka yi musu fyade, yayinda mata 37 kuma suka ce an zambace su an kwana da su bayanda aka yi musu alkawarin bogi na cewa za’a agaza musu da wasu kaya ko ma za’a aure su.
Rahoton yace da yawa daga cikin matan an watsar da su bayanda suka dauki ciki.
Izuwa yanzu dai hukumomin gwamnatin ta Nigeria basu maido da wani martani kan wannan zargin ba.