Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Zai Ayyana Dokar Ta Baci Tare Da Amfani Da Sojoji Kan Iyakar Mexico


Rantsar da sabon Shugaban Amurka na 45 da 47, Donald Trump Janairun 20, 2025
Rantsar da sabon Shugaban Amurka na 45 da 47, Donald Trump Janairun 20, 2025

Shugaban Amurka na 47 din zai fara aiki nan take da jerin umarnin zartarwa da aka tsara domin matukar rage yawan bakin hauren dake shiga kasar.

Donald Trump zai fitar da jerin umarnin zartarwa da zasu fasalta yadda Amurka zata shawo kan batun 'yan kasa da baki, kamar yadda ya bayyana a yau Litinin jim kadan bayan rantsar da shi.

Shugaban Amurka na 47 din zai fara aiki nan take da jerin umarnin zartarwa da aka tsara domin matukar rage yawan bakin hauren dake shiga kasar.

"Da fari, zan ayyana dokar ta bacin kasa akan iyakarmu ta kudu, a cewar Trump.

"Zamu dakatar da shigowa kasarmu ta barauniyar hanya nan take, sannan zamu fara aikin mayar da milyoyin baki masu aikata miyagun laifuffuka zuwa kasashensu da suka fito.

"Zan aika dakaru zuwa iyakarmu ta kudu domin dakile mummunan yunkurin mamaye kasarmu," a cewarsa.

Trump, wanda yayi yakin neman zabe akan dandamalin kawo karshen shigar bakin hauren wanda manufofinsa suka yi shura a tsakanin fafutukar sauya bayanan al'umma, haka yana da niyyar dakatar da dadaddiyar al'adar nan ta baiwa duk mutumin da aka haifa a Amurka iznin zama dan kasa na kai tsaye.

"Zamu kawo karshen samun mafaka," kamar yadda mataimakiyar sakataren yada labaran fadar White House, Anna Kelly ta shaidawa manema labarai, tare da kirkirar tsarin debewa na nan take ba tare da damar samun mafaka ba. Haka kuma zamu kawo karshen tsarin samun iznin zama dan kasa na hakkin haihuwa a wuri."

A karkashin sabuwar dokar, mutane da suka nemi iznin shigowa Amurka daga kan iyakarmu da Mexico ba za'a bari su shigo ba har sai anyi hukunci akan bukatarsu.

"Zamu sake tabbatar da dokar ta"ku zauna a mexico tare da gina ganuwa," a cewarta.

Amurka zata sake kwato matsayinta na zama kasaitacciya kuma kasa mafi karfi da mutunci a duniya, da za'a rika jin tsoro ana kuma kauna a fadin duniya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG